Kakakin hukumar tsaron kasar Sin Yang Yujun ya shedawa manema labaru a ranar alhamis din nan cewa, gwamnatin kasar Sin da sojinta sun yi hadin kai domin tantance allurar rigakafin cutar Ebola, wanda rukunin nazarin kimiyya na kwalejin koyon ilmin kimiyyar aikin jiyya ta kasar Sin ta fitar, kuma ana sa ran gudanar da aikin gwaji akan mutane a wannan wata da muke ciki.
Ban da haka kuma, Yang Yujun ya ce, tun tsakiyar watan Satumba wannan shekarar, sojojin kasar Sin suka tura rukunonin ma'aikatan jiyya da masana da dama da suka hada da mutane kimanin 300 zuwa Saliyo da Laberiya, wuraren da suke fama da Ebola. A cewarsa, wadannan rukunonin sun kafa cibiyar sa ido kan wadanda suke kamu da cutar dake kunshe da gadoji 78 a Saliyo, tare kuma da kafa irin wannan cibiyar a Laberiya dake kunshe da gadoji 100, har ma da kafa tsarin tuntubar juna da wasu manyan hukumomi da kungiyoyi ciki hadda kungiyar kiwon lafiya ta duniya, kungiyar masu aikin jiyya ta maras iyakar kasa, gwamnatocin Saliyo da Laberiya, rundunar kiyaye zaman lafiya ta MDD dake Laberiya da sauransu. (Amina)