in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sinawa masu amfani da yanar gizo da hukumar WFP suna aiki tare don hana yaduwar cutar Ebola
2014-12-23 15:14:08 cri
A jiya ne shirin samar da abinci na duniya wato WFP da asusun taimakawa masu fama da talauci na kasar Sin da kamfanin Tencent na kasar Sin sun kafa wata gidauniyar neman kudi don yaki da cutar Ebola. Jama'a na iya bada tasu gudumawar ta hanyar shiga shafin QQ ta wayarsu ta salula, kuma za a mika kudaden da aka tattara ga WFP don gudanar da ayyukan taimakawa kasashen Guinea da Liberia da Saliyo mafi fama da cutar Ebola da biya bukatun jama'a a fannonin abinci da kiwon lafiya.

Shugaban sashen hulda da kamfanonin kasa da kasa na WFP Jay Aldous ya bayyana cewa, za a yi amfani da kudaden da aka tattara ne wajen taimakawa al'ummomin kasashen yammacin Afirka kan tinkarar cutar Ebola. Kana mataimakin shugaban kamfanin Tencent Yin Yu ya bayyana cewa, kamfaninsa ya shiga aikin tattara kudi, kuma yana fatan za a yi amfani da fasahohin zamani don bada gudummawa ga sha'anin taimakawa mutanen dake cikin mawuyacin hali a duniya. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China