Babban sakataren MDD Ban Ki-moon ya yi kiran da a kara zage damtse a kokarin da ake na sake farfado da kasashen yammacin Afirka da cutar Ebola ta fi kamari.
Ban Ki-moon ya bayyana hakan ne yayin da yake zantawa da manema labarai a hedkwatar MDD bayan rangadin da ya kai kasashen Guinea, Liberia, Saliyo, Mali da kuma Ghana don gane ma idonsa irin ci gaban da aka samu a yankunan da cutar da fi yi wa illa.
Ban ya ce, kamata ya yi kasashen duniya su kara samar da taimakon kudi, ma'aikatan lafiya, kayan aiki da sauran muhimman tallafin da ake bukata ga kasashe da al'ummomin da wannan cuta ta shafa.
Bugu da kari Ban Ki-moon ya ce, wajibi ne a kara kokarin taimakawa yaran da suka rasa iyayen sakamakon wannan cuta.
Alkaluman hukumar lafiya ta duniya na nuna cewa, mutane 18,603 ne suka kamu da cutar a kasashen Guinea, Liberia, Mali, Saliyo da Amurka da kuma kasashen Najeriya da Senegal da Spain da aka samu bullar cutar a baya, yayin da mutane 6,915 suka mutu sanadiyar cutar. (Ibrahim)