Lin Songtian wanda ya bayyana hakan yayin wani taron da aka yi a jami'ar Peking mai taken "Fahimtar cutar Ebola da daukar matakin da ya dace". ya ce, muhimmin abu dake addabar aikin kiwon lafiya a Afrika shi ne rashin samun ci gaba. Ya kara da cewa, ba kawai kasar Sin take mai da hankali a kan taimakawa kasashen Afirka wajen tinkarar cutar ta Ebola da ake fuskanta a yanzu ba, haka kuma tana dora babban muhimmanci kan farfado da kasashen Afrika musamman ma wasu ke fama da cutar, a fannonin kiwon lafiya, tsarin yin rigakafin cututtuka da kara karfin yin rigakafi bayan da aka shawo kan cutar ta Ebola.
Ban da haka kuma, Lin Songtian ya ce, gwamnatin kasar Sin na shirin kafa cibiyar nazarin kwayoyin cuta da shawon kan wasu cututtuka da su kan bullo a wurare mafi zafi a kasashen Afrika, tare kuma da tura masananta da su shiga wannan aiki. Har ila yau, Sin ta mai da aikin hadin kai ta fuskar kiwon lafiya a matsayin daya daga cikin ayyukan da za'a tattauna a wajen taron ministoci na dandalin tattaunawar hadin kai tsakanin Sin da Afrika da za a yi a badi, har ma da kara zuwa jari a wannan fanni.
An ba da labarin cewa, ya zuwa yanzu, yawan kudin da Sin ta kashe wajen tallafawa kasashen Afrikan wajen yaki da Ebola ya kai kudin Sin RMB miliyan 750, wadanda suka shafi kasashen Afrika 13 da MDD, WHO, AU da dai sauran kungiyoyin kasa da kasa. (Amina)