A ganin masanan, akwai isassun na'urori a cibiyar, kuma ana gudanar da ayyuka bisa ka'idojin hukumar WHO, don haka suka yaba da ayyukan da cibiyar ta gudanar.
Ya zuwa ranar 24 ga watan Disamba, cibiyar ta karbi mutane 544 da aka zaton sun kamu da cutar Ebola, yayin da mutane 230 daga cikinsu aka tabbatar sun kamu da cutar, kuma aka kawar da mutane 217 daga cikinsu da ake zaton sun kamu da cutar .(Zainab)