A wannan rana kuma, Ban Ki-moon ya gana da shugaban kasar Mali Ibrahim Boubacar Keita, inda ya nuna yabo matuka dangane da matakan da kasar Mali ta dauka cikin sauri wajen yaki da cutar Ebola.
Bugu da kari, bisa labarin da gwamnatin kasar Mali ta fitar bayan ganawar Ban Ki-moon da shugaban kasar, an ce, a yayin ganawarsu, Ban Ki-moon ya sake yin kira ga shugaba Keita da ya shiga shawarwarin zaman lafiya cikin himma da kwazo, sabo da samun dauwamammen zaman lafiya a kasar Mali ita ce hanya daya kadai da za ta taimaka wa kasar wajen cimma burinta na samun dauwamammen ci gaba.
Kaza lika, jiya Lahadi 21 ga wata da sassafe, rukuni na biyu na tawagogin ba da horo kan yin rigakafi da hana yaduwar cutar Ebola da kasar Sin ta tura zuwa kasar Saliyo sun isa kasar, inda ake fatan za su hada kai da rukunin farko na tawagar da kasar Sin ta tura zuwa kasar don ba da horo ga likitoci da ma'aikatan unguwanni kimanin dubu hudu na kasar kan harkokin kiwon lafiya
Haka kuma, cikin tawagogin da kasar Sin ta tura zuwa kasar Mali akwai masana guda 14 a fannonin yin rigakafi da hana yaduwar cututtuka masu yaduwa, malaman asibiti da dai sauransu. (Maryam)