Mr. Ban ya bayyana hakan ne a jiya Asabar a birnin Conakry hedkwatar kasar ta Guinea, a ziyara irin ta ta farko da ya kai kasar, tun bayan barkewar cutar ta Ebola a kasar.
Da yake jawabi ga taron manema labaru, bayan ganawar sa da shugaba Alpha Condé, Ban ya yi kira ga mahukuntan kasar da su kara jan hankulan al'umma, wajen daukar karin matakan shawo kan yaduwar cutar tare da taimakon kasashen duniya, ko a kai ga cimma nasarar da ake fata.
Ban ya ce har ya zuwa lokacin da za a kai ga shawo kan wannan cuta, MDD za ta ci gaba da marawa kasar ta Guinea baya.
A kwanakin baya ne dai hukumar lafiya ta duniya WHO, ta bayyana cewa cutar Ebola na ci gaba da matukar yaduwa a kasashen Guinea, da Liberiya, da kuma Saliyo.
Kuma ko da yake yawan karuwar mutanen dake kamuwa da ita a yankin Guéckédou na Guinea ya yi matukar raguwa, a hannu guda yankin Masonta dake kudu maso gabashin kasar na fama da karin masu kamuwa da cutar.(Fatima)