An kira taron ma'aikatar kasuwanci ta kasar Sin a wannan rana da safe inda a yayinsa, Gao Hucheng ya nanata cewa, kamata ya yi Sin ta dauki matakin a sabon zagaye don bude kofa ga kasashen waje a shekarar 2015, da mai da hankali kan aikin kirkire-kirkire, da karfafa karfin takara, da tabbatar da bunkasuwar cinikayyar cikin kasar da na waje, da hada kai tsakanin kasa da kasa ta fuskar tattalin arziki.
Mataimakiyar shugaban kwalejin nazari a ma'aikatar kasuwanci ta kasar Sin Madam Xing Houyuan ta nazarci cewa, Sin za ta jawo hankalin kasa da kasa sosai wajen shigo da jari daga kasashen waje a shekarar 2015, lamarin da zai samar da wani yanayi mai kyau a wannan fanni. Matakan da za a dauka za su kyautata halin samun jari da kasahen waje za su zuba a nan kasar Sin tare kuma da samarwa kasashen waje wani sukuni mai kyau wajen zuba jari a kasar Sin, wadannan matakai sun hada da kyautata dokokin dake shafar kamfanonin waje, sassauta ma'aunin shiga sana'ar ba da hidima, da kara bude kofa kan masana'antu da habaka yankin ciniki cikin 'yanci na Shanghai da kafa sabbin yankunan ciniki cikin 'yanci a Tianjin, Guangdong, Fujian, har ma da kara bude kofa a wuraren dake dab da kogin Yangtse, da iyakokin kasar. (Amina)