Kasar Sin na matukar burin ganin an warware takaddamar cinikayya tsakaninta da kungiyar EU ta hanyar tattaunawa, don gane da na'urorin samar da lantarki ta hasken rana da take kerawa.
Firimiyan kasar Sin Li Keqiang ne ya bayyana hakan, da maraicen ranar Litinin 3 ga watan nan na Yuni, yayin wata tattaunawar da ya yi da shugaban hukumar gudanarwar kungiyar ta EU Jose Manuel Barroso ta wayar tarho. Li ya kara da cewa, rashin daukar kwararan matakan warware wannan takaddama, na iya cutar da bangarorin biyu. har ila yau Li ya ce, kasar Sin na adawa da munanan manufofin kasuwanci dake hana ba da damar hada-hadar cinikayya cikin 'yanci.
A nasa jawabi, Barroso ya ce, kungiyar EU ta shirya tsaf domin yin hadin gwiwa da kasar Sin, a fagen tattaunawa da gudanar da shawarwari, domin warware wannan takaddamar cinikayyar da ake batu a kanta. Matakin da a cewarsa zai taimakawa hadin kan bangarorin biyu daga dukkanin fannoni.
A watan da ya gabata ne dai hukumar zartaswar kungiyar tarayyar ta Turai, ta dora harajin kaso 47 bisa dari kan kayayyakin samar da lantarki ta hasken rana, wadanda Sin ke fitarwa zuwa ga kasuwannin Turai, domin dakile abin da EU ke kallo a matsayin wani tsarin kasuwanci na karya farashi.(Saminu)