Yawan kudin shiga da kasar Sin za ta samu wajen shige da ficen kayayyaki zai kai matsayi na farko a duniya
Kwanan baya, a gun taron nazarin batun tattalin arzikin kasar Sin, kakakin ma'aikatar kula da harkokin kasuwanci ta kasa Sin Shen Danyang ya ce, a karshen watanni uku na bana, kasar Sin za ta yi ciniki da kasashen duniya kamar yadda ya kamata, an kimanta cewa, saurin karuwar cinikin tsakanin kasar Sin da kasashen duniya zai kai kashi 8 cikin 100. Ke nan, jimillar kudin da kasar Sin za ta samu wajen shige da ficen kayayyaki za ta kai matsayi na farko a duniya.
Shen Danyang ya ce, bisa kididdigar da hukumar kwastam ta yi a watanni biyu da suka wuce, an ce, yawan cinikin da kasar Sin ta yi da kasashen duniya ya samu kyautatuwa, kuma an raya cinikin da kasar Sin ta yi da kasashen duniya yadda ya kamata a karshen watanni uku na bana. Ya bayyana cewa, manufar raya tattalin arziki daga manyan fannoni za ta sa kaimi ga cinikin da kasashen waje. Sabo da haka, a takaice dai, za a ci gaba da raya tattalin arziki yadda ya kamata a karshen rabin shekarar bana.(Bako)