in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin na sahun gaba a fannin cinikayyar kasa da kasa a shekarar 2013
2014-03-01 17:29:16 cri
Rahotanni daga ma'aikatar kasuwancin kasar Sin sun bayyana cewa, wata kididdigar da ofishin sakataren kungiyar cinikayya ta WTO ta yi, ya nuna cewa kasar ta Sin ce ke kan gaba a fannin cinikayyar hajoji tsakanin kasa da kasa a shekarar 2013.

Kididdigar da aka fitar a yau Asabar 1 ga watan nan na Maris, ta kuma ce cinikayyar kasa da kasa da kasar Sin ta yi a shekarar 2013, ta kai ta dallar Amurka biliyan 4160, yayin da na kasar Amurka, wadda ta taba kasance gaba a wannan fanni a shekaru da dama, ya tsaya a dallar Amurka biliyan 3910. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China