in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin na tabbatar da tsarin yankin ciniki cikin 'yanci yadda ya kamata
2014-06-22 16:59:22 cri

Wani rahoton mahukuntan dake lura da manufar cinikayya cikin 'yanci a birnin Shanghai dake gabashin Sin ya nuna cewa, wasu birane da lardunan dake dab da tekun Sin ciki hadda Guangdong, da Tianjin na bada himma da gwazo wajen shiga wannan tsari.

Rahoton ya kuma nuna cewa akwai wasu karin birane dake da nisa da teku, wadanda su ma ke nuna sha'awa kwarai kan wannan tsari a bana. An bayyana cewa cikin watanni 6 na farkon wannan shekara ta 2014, wannan tsari na kafa yankin ciniki cikin 'yanci ya samu gagarumar nasara.

Wata kididdiga ma ta nuna cewa, a wannan shekara da muke ciki za a mika bukatar kara kafa wasu yankunan cinikayyar cikin 'yanci fiye da 20. Ko da yake a hannu guda, kwamitin tsakiyar jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin, ya shawarci wurare daban-daban, da su yi tunani mai zurfi kan hakan kafin su dauki mataki na gaba.

Yanzu haka dai ana gudanar da wannan manufa ta yankin ciniki cikin 'yanci a birnin Shanghai yadda ya kamata, musamman a fannonin yiwa harkar hada-hadar kudi kwaskwarima, da aikin kirkire-kirkire, ana kuma tabbatar da wasu matakai, da wasu ma'aunan hukumomi suka gabatar, ciki hadda bankin jama'ar kasar Sin, da hukuma mai sa ido kan ayyukan bankuna ta kasar Sin CBRC, da hukumar dake lura da takardun hada-hadar kudi ta kasar Sin, da hukumar kula da sashen inshora ta kasar Sin.

A fannin hada-hadar kasa da kasa kuwa, kasar Sin ta gudanar da shawarwari kan yankin ciniki cikin 'yanci a kasashe makwabtanta, inda a yayin gudanar da shawarwari karo na 11 tsakanin Sin da Korea ta kudu kan wannan aiki, aka kammala shawarwari karo na 4 tsakanin Sin da Japan, da Korea ta kudu. Matakin da ya baiwa bangarorin uku damar cimma matsaya guda kan wasu batutuwa, ciki hadda harajin cinikayya.

Bugu da kari mahukunta na kokarin bunkasa wannan manufa ta yankin ciniki cikin 'yanci, tsakanin Sin da kungiyar tarayyar kasashen kudu maso gabashin Asiya ta (ASEAN). Baya ga burin da ake da shi, na tattaunawa tsakanin Sin da yankin Macau kan wannan batu. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China