Bisa kididdigar da aka samu, an ce, a shekarar 2012, yawan cinikin shige da fice da aka yi tsakanin kasar Sin da kasashen da ke samun bunkasuwa sosai da kasashe masu tasowa ya samu habaka cikin sauri, idan aka kwatanta wannan adadi da na shekarar 2007, yawan cinikin shige da fice ya karu da kashi 6.2 cikin 100, cikinsu, yawan kudaden da kasar Sin ta samu wajen yin cinikin shige da fice da kasar Brazil ya karu da kashi 188.5 cikin 100, yayin da yawan cinikin da ke tsakaninta da Rasha ya karu da kashi 83 cikin 100, ban da wannan kuma, yawan cinikin da ke tsakanin kasashen Sin da India ya karu da kashi 72 cikin 100, kuma, yawan cinikin shige da fice da ke tsakanin Sin da Afrika ta kudu ya karu da kashi 327 cikin 100.(Bako)