in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta gabatar da manufofin tabbatar da zaman karko game da karuwar cinikin ketare
2014-05-15 16:24:29 cri
A yau Alhamis 15 ga wata ne, ofishin majalisar gudanarwar kasar Sin ya gabatar da manufofi guda 16 da nufin tabbatar da zaman karko game da karuwar cinikin ketare, wannan shi ne karo na biyu da majalisar gudanarwar kasar ta fitar da manufofin dake shafar harkokin ba da tabbaci kan karuwar cinikin ketare cikin shekaru biyu da suka gabata.

An fitar da wadannan manufofi ne kan fannonin hudu da suka hada da, na daya, kyautata tsarin da ake bi wajen gudanar da cinikin ketare, na biyu, ci gaba da kyautata yanayin cinikin ketare, na uku, karfafa manufofin da abin ya shafa don gudanar da harkokin cinikin ketare yadda ya kamata, kana na hudu, karfafa kwarewar kamfanonin cinikin ketare ta yadda za su iya gudanar da ayyukansu lami lafiya. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China