in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yawan cinikin shigi da fici a kasar Sin ya karu kashi 9.3 bisa dari a watan Nuwanba
2013-12-09 15:55:26 cri

Bisa kiddidigar da babbar hukumar kwastan ta kasar Sin ta bayar a ran 8 ga wata, an ce, a watan Nuwamba, kudin cinikin shigi da fici da Sin ta samu ya kai dalar Amurka biliyan 370 da miliyan 610, wanda ya karu da kashi 9.3 bisa dari idan aka cire tisiri daga canzawar darajar kudin Sin.

Hukumar ta ce, yawan kudin kayayyakin da Sin ta fitar zuwa ketare ya kai kudin dala biliyan 202 da miliyan 210, wato wannan shi ne karo na farko da ya wuce dala biliyan 200, wanda ya karu da kashi 12.7 bisa dari, har wa yau kudin da aka samu daga cinikin kayayyakin da aka shigo da su ya kai dala 168 da miliyan 400, wanda ya karu da kashi 5.3 bisa dari.

Kwararru kan harkar tattalin arziki sun nuna cewa, ana samu kyautattuwar tattalin arziki a duk duniya, kuma kasashen Amurka da Turai sun shiga cikin yanayi mai kyau na sayen kayayyaki saboda murnar bikin kirsimati, an kuma samu kyakkyawan sakamako daga manufofin da kasar Sin take gudanarwa na tabbatar da karuwar fitar da kaya zuwa ketare, wadannan dalilai ne suka kai ga karuwar cinikin shigi da fici da Sin ta samu a watan Nuwamba.(Danladi)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China