Mr Shen ya ce tafiyar hawainiyar da kasar ta fuskanta a bangaren cinikayyar ketare a watan Mayu, ya faru ne sakamakon dokokin da gwamnati ta bullo da su da nufin rage kudaden da ke kewaya a kasuwa da ake fakewa da sunan biyan kudaden cinikayya.
Ya ce karuwar darajar kudin kasar na Yuan da raguwar bukatun kayayyaki daga ketare, sun yi tasiri kan kayayyakin da ake fitarwa zuwa ketare, don haka ana ganin cewa, karuwar cinikayyar ketaren kasar a wannan shekara ba za ta yi wani tsanani ba. (Ibrahim)