Bugu da kari, cikin watanni bakwai da suka gabata na shekarar bana, adadin kudaden da Sin ta samu wajen shige da fice ya kai yuan biliyan dubu 14.72, wanda ya karu da kashi 0.2 bisa dari bisa na makamancin lokacin shekarar bara, kuma an samu rarar kudi yuan biliyan 924.9, adadin da ya karu da kashi 18 bisa dari.
A bangaren abokan cinikayya kuma, a wadannan watanni bakwai da suka gabata, jimillar cinikayyar dake tsakanin Sin da Turai ta karu da kashi 10 bisa dari, yayin da jimillar ta karu da kashi 3.9 bisa dari a tsakanin Sin da Amurka, sai kuma kashi 3.5 bisa dari da aka samu a tsakanin Sin da kungiyar tarayyar kasashen kudu maso gabashin nahiyar Asiya. (Maryam)