Ranar Alhamis 17 ga wata, a nan birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin, kakakin ma'aikatar kasuwancin kasar Sin mista Shen Danyang ya yi tsokaci kan raguwar saurin karuwar ciniki da kasashen waje da kasar Sin ta yi a watan Satumba da ya wuce, inda ya ce, dalilin da ya sa haka shi ne karancin bukatu da aka samu sakamakon tafiyar hawainiya da tattalin arzikin sabbin kasuwanni ya yi. Amma duk da haka, a cewar mista Shen, ana sa ran ganin dan karuwar yawan kayayyakin da kasar Sin za ta fito da su a watanni 3 na karshen shekarar 2013, har ila yau kuma, farfadowar tattalin arzikin Sin za ta sanya kasar ta kara shigo da kayayyaki daga kasashen waje sosai.
Ban da haka, alkaluman ma'aikatar kasuwancin kasar Sin sun nuna cewa, tsakanin watan Janairu da na Satumban bana, yawan jarin waje da kasar ke amfani da shi yana ta karuwa cikin watanni 8 a jere. Hakan, a ganin mista Shen, ya sheda cewa, masu zuba jari suna da cikakken imani kan tattalin arzikin kasar Sin, don haka jimilar kudin nan ba za ta yi fadi tashi sosai a bana ba. (Bello Wang)