in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ba za ta hana kamfanonin ketare shigowa kasar ba
2014-09-08 16:43:32 cri
A yau Litinin 8 ga wata ne, aka bude taron karawa juna sani kan harkokin zuba jari na kasa da kasa na shekarar 2014 a birnin Xiamen na kasar Sin, kuma wannan taro wani bangare ne na taron tattaunawar harkokin ciniki da zuba jari a kasashen waje na kamfanonin kasar Sin karo na 18.

Mataimakin firaministan kasar Sin Wang Yang ya halarci bikin bude taron, inda ya bayyana cewa, kasar Sin ba za ta canja tsarinta na zuba jari cikin hadin gwiwa ba.

Ya ce, kasar Sin za ta ci gaba da habaka wannan tsari, haka kuma, yanayin zuba jari cikin hadin gwiwa a nan kasar Sin na ci gaba da samun kyautatuwa. A halin yanzu, gwamnatin kasar Sin na dukufa wajen kyautata yanayin cinikin kasar, ta yadda zai dace da ka'idojin kasa da kasa, kuma Sin tana karfafa dokokin da abin ya shafa yadda ya kamata. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China