Cibiyar nazarin hada-hadar saye da sayarwa a kan Intanet a kasar Sin ta ba da wani rahoto a ranar Laraba 20 ga watan nan, wanda ke nuna cewa yawan kudin da cinikayyar saye da sayarwa a kan Intanet ke samarwa, ya kai kimanin dala biliyan 1263 a shekarar 2012 da ta gabata, adadin da ya karu da kashi 30.83 cikin dari bisa na shekarar 2011.
Daga cikin wannan adadi, yawan kudin da ya shafi ciniki tsakanin kamfanoni daban-daban a wannan fanni ya kai dala biliyan 1000, yayin da yawan kudi da ya shafi cinikayyar kayayyakin da ba na sari ba ya kai kimanin dala biliyan 212.3, dukkansu sun karu bisa na shekarar 2011.
Rahoton ya ce, wannan irin sha'ani ya zama sabon karfin raya tattalin arzikin kasar Sin, tare da samar da karin guraben aikin yi. Ya zuwa karshen shekarar 2012, yawan mutane da suka samu aikin yi a wannan fanni ya kai fiye da miliyan 2, yayin da mutane fiye da miliyan 15 suka samu aikin da ya shafi wannan sana'a. (Amina)