Har kullum sabunta kayayyaki na sa kaimi kan bunkasuwar masana'antu. A yayin taron baje-kolin da ake yi a Guangzhou, an gano cewa, wasu masana'antu sun tabbatar da makasudinsu a kasuwa sosai, tare da kulawa da salon zamani a duniya, sun yi ta fitar da wasu kayayyaki na yayi, wadanda suka samu karbuwa a kasuwa.
A kokarin kara sai da kayayyaki zuwa ketare, wadanda suka biya bukatun masu sayayya, wasu masana'antu sun aika da kwararru a fannin kasuwanci a wurin gudanar da taron don tattaunawa da masu sayayya kai tsaye, lamarin da shi ma ya samu sakamako mai kyau. (Tasallah)