Shugaba Xi yace aikin kuma zai sa kaimi ga bunkasuwar tattalin arziki da al'ummar Sinawa cikin dogon lokaci, tare da ba da tabbaci ga aikin kyautata zaman rayuwar jama'a. Ya lura da cewa bayan kokarin da ma'aikata fiye da dubu 100 suka yi, an fara jigilar ruwa a tsakiyar kasa, wannan aikin abu ne da ya alamanta cewa, an cimma burin jigilar ruwa a gabas da kuma tsakiyar kasar.
Matakin kuwa, a cewa Shugaba Xi ya zama wani babban ci gaban da Sin ke samu cikin tsarin yin kwaskwarima da bude kofa ga kasashen waje da raya kasa bisa tsarin dake dacewa da zamani mai halayen musamman na gurguzu na kasar Sin. Daga nan sai Mr Xi ya bayyana kyakkyawar fata da taya murnar ci gaban da aka samu, tare kuma da jinjina ma al'ummar da suka bautawa wannan aiki. (Amina)