Firaministan Fiji Josaia Voreqe da uwargidansa ne suka tarbi shugaba Xi da mai dakinsa a filin saukar jiragen sama na Nadi.
A jawabinsa shugaba Xi ya ce, yana duba hanyoyin hadin gwiwa da za su tattauna da shugabannin kasar Fiji, wadanda za su bunkasa dangantakar kasashen biyu a nan gaba.
Bugu da kari a lokacin da yake Fiji, shugaba Xi zai gana da shugabannin tsibiran kasashe 8 da suka kulla huldar diflomasiya da Sin don tattauna hanyoyin zurfafa hadin gwiwa da samun moriya tare.
Shugaba Xi ya ce, Sin na daukar tsibiran kasashen a matsayin abokai na kwarai kuma za su yi aiki tare don inganta makomar dangantakarsu a nan gaba.
Ya kuma jaddada kudurin kasar Sin na goyon bayan al'ummar kasashen tsibiran a kokarin da suke yi na samun bunkasuwar da za ta dace da su, kiyaye cikakkun yankuansu da 'yancinsu da kuma muradunsu, sannan su shiga a dama da su a harkokin kasa da kasa da na shiya-shiya kamar sauran kasashe. (Ibrahim)