in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Sin ya gabatar da wani sharhi yayin ziyararsa a New Zealand
2014-11-19 15:54:09 cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da wani sharhi da aka buga a jaridar The New Zealand Herald mai taken "Kara hadin gwiwa tsakanin Sin da New Zealand".

Sharhin wanda shugaba Xi ya gabatar a ran 19 ga watan nan, ya bayyana kasar Sin da New Zealand, a matsayin kasashen dake samun ci gaba sosai, a fannin raya dangantakar dake tsakaninsu. Musamman ta yadda Sin ta zama kasa dake matsayin farko ga New Zealand ta fuskar ciniki da kuma yawan dalibai dake karatu a kasar.

Ban da haka, New Zealand ta zama kasa mai wadata ta farko da ta kulla yarjejeniyar cinikayya maras shinge da kasar Sin. Hakan ya sa hadin gwiwar sassan 2 ke haifar da babban alfanu ga jama'ar kasashen, musamman ta fannin samar da yawan kayayyaki masu araha, da karin guraben aikin yi, kana da zarafi mai kyau na samun ilmi da yin musaya.

Dadin dadawa, sharhin ya nuna cewa, mutunta juna, da nuna daidaito sun zama muhimman jiguna ga bunkasuwar dangantakar dake tsakanin kasashen biyu. Yayin da koyi da juna, da haifar da moriya ga juna suka zama babban karfin dake ingiza hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu.

Kaza lika samun kwarin gwiwar kasancewa a sahun gaba a fagen kirkira, da daukar dukkanin nauyi tare, da sanin muhimman bambance- bambance dake tsakanin sassan biyu, ya sa dangantakar dake tsakanin kasashen biyu zama abin koyi ga dangantakar dake tsakanin kasar Sin mai tasowa, da kuma New Zealand mai wadata.

Bugu da kari hakan ya sa dangantakar dake tsakanin kasashen biyu zama abin koyi ga sauran kasashen duniya. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China