in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaba kasar Sin ya yi kira da a kara ilimantar da jama'a game da tsarin mulkin kasa
2014-12-03 20:36:58 cri
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi kiran da a kara ilimantar da jama'a game da tsarin mulkin kasa ta yadda jama'a za su kara fahimtar rawar da dokoki ke takawa.

Shugaban ya bayyana hakan ne gabanin ranar kaddamar da tsarin mulkin kasa da za a yi gobe Alhamis.

Ya ce, tsarin mulkin kasa shi ne tafarkin da kasa ke bi wajen tafiyar da harkokinta,kuma ya kunshi manufofin jam'iyya da na jama'a. Sannan tsarin mulkin kasar Sin ya dace da yanayin kasar Sin da manufofinta da ci gaban da ta samu a wannan lokaci.

Shugaba Xi ya ce, tsarin mulkin kasa ya kasance jagora ga jam'iyya mai shigar gurguzu na kasar Sin, don haka wajibi ne a tafiyar da harkokin kasa bisa doka.

Ya ce, kamata ya yi a yi amfani da wannan rana wajen ilmantar da jama'a game da dokokin kasa, ta yadda za a aiwatar da dokoki yayin tafiyar da harkokin mukin kasa don taka rawar da ta dace wajen ciyar da shirin yin kwaskwarima da doka gaba.

A ranar 1 ga watan Nuwamba ne majalisar zartaswar kasar ta kebe wannan rana, a kokarin ganin ana tafiyar da harkokin mulkin kasa bisa doka. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China