in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping ya gana da shugabannin kasashen tsibiran Pacific
2014-11-22 20:28:37 cri
A ranar Asabar din nan ne shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da shugabannin kasashen tsibiran Pacific a birnin Nadi na kasar Fiji.

Tattaunawar da shuwagabannin suka gudanar ta ba su damar zantawa kan harkokin da suka shafi ci gaban kasashensu, inda suka cimma matsaya guda game da kafa dangantakar kawance bisa manyan tsare-tsare bisa ka'idojin mutunta juna da kuma neman ci gaba cikin hadin gwiwa.

Shugaba Xi wanda ya jagoranci wannan taro ya gabatar da jawabi game da manufofin kasar Sin a fannin zurfafa dangantaka da kasashen tsibiran Pacific, ya kuma jaddada cewa, kasar Sin aminiya ce ta hadin gwiwa da kasashen tsibirai.

Kaza lika shugaban kasar ta Sin ya bayyana aniyar kasarsa ta kara mai da hankali kan bunkasa dangantaka tsakanin Sin da kasashen tsibiran Pacific. Game da hakan, shugaba Xi ya gabatar da wasu shawarwari biyar, da suka hada da bukatar kulla dangantakar abokantaka bisa ka'idojin girmama juna da neman ci gaba tare.

Ta biyu ya ce ya dace a karfafa shawarwari tsakanin manyan shugabannin kasashen. Sai batun zurfafa hadin gwiwar kasashen yadda ya kamata. Shawara ta hudu kuwa ita ce batun habaka shawarwari ta fuskar musayar al'adu. Sai shawara ta biyar da ta shafi karfafa hadin gwiwar kasashen a fannoni daban daban.

A nasu bangare, shugabannin kasashen tsibiran Pacific sun nuna matukar amincewarsu ga shawarar gina dangantakar abokantaka da kasar Sin bisa ka'idojin mutunta juna da neman ci gaba tare, sun kuma bayyana cewa, jama'arsu na fatan koyi daga fasahohin kasar Sin wajen neman bunkasuwa, da karfafa shawarwarin dake tsakaninsu da kasar Sin bisa fannoni daban daban, da kuma zurfafa zumunta, ta yadda ko wace kasa za ta iya cimma burinta bisa hadin gwiwa tare. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China