Shugaba Xi ya bayyana hakan ne lokacin da yake jawabi a taro karo na 7 na babban kwamitin yin gyare-gyare na kasar da aka gudanar yau Talata a nan birnin Beijing, inda ya tabo batun yadda ake samun fahimtar juna tsakanin masu tsara manufofin yin gyare-gyare da yadda ake aiwatar da shirin a yankunan karkara.
Ya ce, wajibi ne hukumomin su mayar da hankali kan batutuwan da suka fi shafar jama'a da batutuwa masu wuyar sha'ani a rayuwar jama'a ta yadda za a tsara hanyoyin tunkarar wadannan batutuwa daga tushe yayin da ake aiwatar da yin kwaskwarima.
Taron na yau wanda ya kuma tattauna batun yin kwaskwarima kan tsarin mallakar filaye da gidaje da kuma bullo da tsarin gina cibiyoyin al'adu na zamani ya samu halartar manyan shugabannin kasar Sin da suka hada da firayin minista Li Keqiang, Liu Yunshan da kuma Zhang Gaoli. (Ibrahim)