Shugaba Xi wanda ya bayyana hakan cikin jawabin da ya gabatar a taron karawa juna sani game da huldar kasashen waje, wanda aka gudanar a ranekun Juma'a da Asabar.
Xi ya jaddada muhimmancin zaman lafiya, da moriyar juna, tare da cimma burikan kasar Sin na bunkasuwa da na tsaro. Yana mai cewa akwai bukatar cimma daidaito a wadannan fannoni.
Kaza lika shugaban kasar ta Sin ya nuna bukatar ci gaba da habaka nasarorin da ake samu na sabunta kasa, da daukaka matsayin Sin, tare da samar da kyakkyawan yanayi da bunkasar huldodin da za su inganta dangantakar Sin da gamayyar kasa da kasa.
"Za mu ci gaba da bin hanyar wanzar da zaman lafiya irin tamu, tare da dogara da kanmu wajen neman bunkasuwa, a yayin da muke ci gaba da ginin kasarmu. Ba za mu kuma taba watsi da hakkokinmu, ko burikan da muka sanya a gaba ba, haka kuma ba za mu bari a dakile manyan manufofinmu ba", a kalaman Shugaba Xi.
Shugaban na kasar Sin ya kuma ce kasarsa za ta ci gaba da goyon bayan dimokaradiyya cikin harkokin diflomasiyya, tare da martaba daukacin manyan manufofin wanzar da zaman lafiyar nan biyar.
Daga nan sai ya sake nanata aniyar Sin ta martaba ikon kasashen duniya na gudanar da mulkin kai bisa ra'ayin al'ummunsu, da hadin gwiwar samar da ci gaba tare, ba tare da la'akari da girma ko karfin kasashen ba. (Saminu Alhassan)