in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi shawarwari a tsakanin shugabannin Sin da Afirka ta Kudu
2014-12-04 21:28:40 cri

A yau ne, shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya yi shawarwari da takwaransa aiki na kasar Afirka ta Kudu Jacob Zuma a nan Beijing, inda shugabannin 2 suka tsara manufar raya huldar da ke tsakanin kasashen 2 daga dukkan fannoni, tare da tsai da kudurin raya huldar da ke tsakanin kasashen 2 zuwa dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare kuma daga dukkan fannoni, da nufin amincewa da juna ta fuskar siyasa, don samun moriyar juna ta fuskar tattalin arziki, su yi koyi da juna ta fuskar al'adu, su kuma taimakawa juna ta fuskar tsaro.

Ban da haka kuma, a yayin shawarwarin, shugaba Xi ya nuna cewa, kasar Sin tana son inganta hadin gwiwa da Afirka ta Kudu wajen kara azama kan shimfida zaman lafiya, kwanciyar hankali da bunkasuwa a nahiyar Afirka.

A nasa bangaren kuma, shugaba Zuma ya ce, kasashen Afirka na fata tare da yin maraba da kasar Sin da ta kara taka rawa wajen samun zaman lafiya da bunkasuwa a Afirka, sannan kasar Afirka ta Kudu na son hada kai da kasar Sin domin kawo alheri ga kasashen Afirka. (Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China