Xi Jinping ya dawo birnin Beijing bayan kammala halartar taron koli na kungiyar G20 da ziyarar da ya kai kasashen Australia da New Zealand da kuma Fiji
A jiya Lahadi ne shugaban kasar Sin Xi Jinping ya dawo birnin Beijing bayan ya kammala halartar taron koli na kungiyar G20 karo na 9 da kuma ziyarar da ya kai a kasashen Australia da New Zealand da Fiji da kuma ganawar da ya yi da shugabannin kasashen tsibiran tekun Pasific da suka kullar dangantakar diplomasiyya da kasar Sin.
A jiya da safe ne, Xi Jinping ya tashi daga kasar Fiji don dawowa nan kasar Sin, inda jama'ar kasar Fiji da dama suka yi ban kwana ga Xi Jinping. A filin jiragen saman kasar kuwa, firaministan kasar Fiji Josaia Uoreque Bainimarama ya shirya wani biki don yin ban kwana ga Xi Jinping. Shugaba Xi Jinping da matarsa sun musabaha da ban kwana ga shugaban kasar Fiji da matarsa, firaministan kasar da matarsa da kuma manyan jami'an kasar. (Zainab)