in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping ya mika sakon murnar taron goyon baya ga al'ummar Palesdinu
2014-11-25 16:29:03 cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aike da sakon taya murnar taron tunawa da ranar goyon baya ga jama'ar Palesdinu, wanda MDD ta gudanar a jiya Litinin.

Cikin sakon na shugaba Xi, ya ce tarihi ya nuna cewa, karfin tuwo ba zai taba haifar da zaman lafiya ba, kuma hawa teburin shawarwari ita ce hanya daya tilo ta warware ko wane irin matsaloli.

Shugaba Xi ya kara da cewa, kasar Sin na fatan Palesdinu da Isra'ila da su gaggauta sake gudanar da shawarwari na shimfida zaman lafiya, domin kawo karshen rigingimu, da kuma wanzuwar zaman karko tsakanin al'ummunsu. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China