in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasashen Sin da New Zealand sun bunkasa matsayin hadin gwiwar da ke tsakaninsu
2014-11-20 20:33:49 cri
A yau ne kasasshen Sin da New Zealand suka yanke shawarar daga matsayin hadin gwiwar da ke tsakaninsu bisa manyan tsare-tsare.

An cimma shawarar daga matsayin hadin gwiwar kasashen biyu ne yayin da shugaba Xi na kasar Sin wanda ke ziyara a kasar ke tattaunawa da firaministan kasar New Zealand John Key.

Shugaba Xi ya ce, yana fatan za a cimma bunkasuwar cinikayya tsakanin sassan biyu wadda za ta kai dala biliyan 23.5 ya zuwa shekarar 2020. Sannan kamata ya yi kasashen biyu su kara bunkasa hadin gwiwa a bangarorin aikin gona da kiwon dabbobi, hada-hadar kudi, fasahar watsa labarai, adana makamashi, kare muhallai da samar da magunguna ta hanyar amfani da tsirrai.

A nasa bangare Mr Key ya yaba da ci gaban da aka samu a hadin gwiwar kasashen biyu tun lokacin da suka kulla huldar diflomasiya shekaru 42 da suka gabata, kuma tun wannan lokaci sassan biyu suka kasance abokan juna na kwarai. Ya ce, New Zealand tana son yin aiki tare da Sin don kara bunkasa hadin gwiwar da ke tsakaninsu, kuma za ta ci gaba da baiwa Sin goyon baya kan batutuwa da suka shafi muhimman muradunta. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China