in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Sin ya fara ziyarar aiki a kasar New Zealand
2014-11-20 10:05:03 cri

  Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya isa birnin Auckland na kasar New Zealand, don fara ziyarar aiki bisa gayyatar shugaban gwamnatin kasar Jerry Mateparae da firaminista John Key.

Firaministan kasar da uwar gidansa, da kuma shugaban birnin Auckland, tare da daya daga manyan jami'an gwamnatin kasar din David Walker ne suka taryi Shugaba Xi da uwar gidansa Madam Peng Liyuan cikin farin ciki.

Da yake jawabi jim kadan da isar sa kasar shugaba Xi ya mika cikakkiyar gaisuwa da fatan alherin sa a madadin jama'ar kasar Sin ga al'ummar New Zealand, yana mai cewa, dangantakar kasashen biyu na samun matukar ci gaba, cikin shekaru 42 da kafuwar huldar diplomasiyya tsakanin su. Ya ce hakan ya haifarwa jama'ar kasashen biyu matukar alfanu, tare da taka muhimmiyar rawa, wajen tabbatar da zaman lafiya, da karko, da wadata a yankin Asiya da tekun Pasific.

Kaza lika shugaba Xi ya yi fatan kara hadin gwiwa da shugabannin kasar New Zealand, da bangarorin daban-daban na al'ummar kasar, don fitar da wani managarcin tafarki, da zai taimaka wajen raya dangantakar dake tsakanin bangarorin biyu, ta yadda ziyarar ta sa a wannan karo, za ta zamo hanyar kara aminci a fannin siyasa, da karin hadin gwiwa, da zurfafa zumunci tsakanin jama'ar kasashen biyu. (Amina)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China