Sanawar ta ce, a makon da ya shude, kungiyar Al-Shabaab ta kai jerin hare-hare kan fadar shugaban kasar, ginin majalisar dokoki da 'yan majalisu a Mogadishu babban birnin kasar. Haka kwamitin ya la'anci wadannan laifufuka tare da mika ta'aziyya ga iyalan mamata da fatan samun sauki ga wadanda aka jikkata.
Sanarwar kuma ta nuna cewa, kwamitin ya jaddada cewa, ko wani irin ta'addanci, barazana ce mai tsanani ga zaman lafiya da tsaron duniya, kuma aikata shi babban laifi ne, dole mai aikata shi ya fuskanci doka. (Amina)