Cikin wata sanarwa, Atom ya ce ya yanke wannan shawara ne duba da rashin amincer sa da manufofin kungiyar da na shugabannin ta.
Tuni dai fadar gwamnatin kasar ta bayyana farin ciki da wannan mataki, ta na mai fatan hakan zai sanya karin dakarun kungiyar ajiye makamai, tare da rungumar shirin wanzar da zaman lafiya da lumana a kasar.
A baya bayan nan dai jagororin kungiyar na tsananta hare-haren da suke kaddamarwa a yankunan jihar Puntland dake Arewa maso Gabashin kasar. Musamman ma yankin tsaunin Galgala da ya zamo sansanin kungiyar tsahon shekaru. (Saminu Alhassan Usman)