Shugaba Mohamaoud ya yi maraba tare da nuna godiya ga kasar Sin da ta sake bude ofishin jakadancinta dake kasar Somaliya, kana ya bayyana cewa, zai ci gaba da samar da yanayin da ya dace ga ofishin jakadancin Sin.
Kasar Somaliya ita ce kasa ta farko da ta kulla dangantakar diplomasiyya a tsakaninta da kasar Sin a yankin gabashin Afirka. Bayan da kasar Somaliya ta fara shiga yakin basasa a shekarar 1991, sai Sin ta janye dukkan jami'ai da ma'aikatan ofishin jakadancinta daga kasar ta Somaliya.
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hong Lei ya sanar a ranar 30 ga watan Yuni na bana cewa, Sin ta tsaida kudurin sake bude ofishin jakadancinta dake kasar Somaliya ne da nufin kara inganta dangantakar abokantaka a tsakaninta da Somaliya.(Zainab)