Binciken da ofishin na tsaron abinci da samar da abinci mai gina jiki ya aiwatar ya ce halin da ake ciki a Somaliya ya karui ne sakamakon karancin ruwan sama,raguwar tallafin jin kai da ake baiwa kasar, da rashin abinci mai gina jiki,tashe tashen hankula da hauhawar farashin kayayyakin masarufi.
Ofishin da kuma cibiyar bayar da gargadi a kan fari sun yi kiyasin cewa tun daga watan fabrairu kusan mutane 857,000 suke cikin kangin tashin hankali da neman taimakon gaggawa abinda ya nuna bukatar da ake dashi na samar da agajin gaggawa. (Fatimah Jibril)