Rundunar 'yan sandan kasar Somaliya ta tabbatar da cewa, wasu dakaru sun kai farmaki kan fadar shugaban kasar dake Mogadishu, babban birnin kasar a ran 8 ga wata. Ta ce, dakarun sun yi amfani da boma-bamai da suka dasa cikin wata mota ne wajen tarwatsa kofar fadar shugaban kasar. Kana, wani jami'in gwamnatin kasar Somaliya ya bayyana cewa, shugaban kasar Sheikh Sharif Sheikh Ahmed ba ya cikin fadar a lokacin da aka kai harin.
Ya zuwa yanzu, babu wani bayani game da wanda ya rasu ko ya jikkata cikin harin, amma bisa rahotannin da kafofin watsa labaran kasar suka bayar, an ce, wasu sun ga wasu gawawaki a cikin da kuma kewayen fadar.
Daga bisani, kungiyar Al-Shabaab ta Somaliya ta sanar da daukar alhakin kai harin. (Maryam)