Mataimakin ministan kudin kasar Sin Shi Yaobin, ya yi kira ga bankin duniya, da ya baiwa kasashe masu tasowa dukkanin gudummawar da ta dace, domin tabbatar da bunkasuwar tattalin arzikin duniya baki daya.
Mr Shi ya nuna cewa, halin da duniya ke ciki na samun bunkasuwa na fuskantar sauye-sauye, abin da ya baiwa kasashe masu tasowa sabbin kalubaloli. Yace ya dace bankin duniya ya yi amfani da ikon sa ta fuskar samar da kudade, da tsarin tattara kudi, ya kuma bullo da sabbin tsare-tsare, tare da jan hankulan masu ruwa da tsaki, wajen samar da kyakkyawan yanayin bunkasar irin wadannan kasashe, ta yadda za a samu zarafin habakar tattalin arzikin duniya bai daya.
Mr Shi wanda ya bayyana hakan a ranar Asabar, yayin taron da bankin duniya, da bankin bada lamuni na IMF suka gudanar ya kara da cewa, a halin yanzu Sin na samun bunkasuwar tattalin arziki yadda ya kamata, kuma ta na samun ci gaba kwarai a fagen kyautata tsare-tsaren ta.
Har wa yau kasar ta Sin, ta na da burin cimma kaso 7.5 bisa dari a fannin ci gaban tattalin arziki a halin da take ciki, ba kuma ta gaggawa samun bunkasuwa. Ya ce mihimmin aiki da take gudana shi ne, samar da yanayi mai kyau na kyautata tsarinta, tare da yin kwaskwarima.
Dadin dadawa, Mr Shi ya ce, bunkasuwar masan'antu da bunkasa garuruwa da birane, za su samar da nasarori da dama, ciki hadda taimakawa samun bunkasuwa a nan gaba. A sa'i daya kuma, tsare-tsaren da aka kyautata a fannin kudi, za su bayar da gudunmawa, wajen kaucewa hadarin asarar dake tattare da hada-hadar kudade. Yayin da kuma kwaskwarimar da Sin ke yi, ke taka muhimmiyar rawa wajen sa kaimi ga bunkasuwarta, dama dukkacin daukacin fadin duniya baki daya.
Wannan ne dai karo na 89, da bankin duniya, da hadin gwiwar asusun ba da lamuni na IMF suka kira taron ministocin kwamitin samun bunkasuwa, taron da aka gudanar a birnin Washington na kasar Amurka. (Amina)