Ya ce, bunkasuwar tattalin arzikin kasar na samun daidaito tsakanin yankuna daban daban tare da taimakawa wajen raya yankuna masu fama da talauci, wadanda suka hada da fasahohin musamman irin na kasar Sin wajen kawar da talauci. Cikin 'yan shekarun da suka gabata, gwamnatin kasar Sin ta zuba jari mai tarin yawa a yammacin kasar, matakin ya ba da babbar gudummawa wajen raya wannan yanki.
Mr. Liu ya kuma bayyana cewa, idan za a iyar ci gaba da yin kwaskwarima bisa dukkan fannoni a kasar Sin, ciyar da aikin raya tattalin arzikin kasa gaba, gudanar da ayyukan da suka shafi daidaituwar kudaden shiga, samar da alheri ga zaman rayuwar jama'a, daidaita matsalar karuwar yawan tsofaffi bisa ga yawan mutanen kasar Sin da dai sauransu yadda ya kamata, to, kasar Sin za ta iya ci gaba da samun bunkasuwar tattalin arziki. (Maryam)