A gun taron manema labaru da aka yi a wannan rana, direktan sashen kula da saka jari da masana'antu na hukumar UNCTAD Zhan Xiaoning ya bayyana cewa, yawan jarin kai tsaye da aka jawo a gamayyar kasashe masu tasowa a shekarar 2013 ya kai kaso 52 daga cikin duk jarin da aka saka, kuma yawansu ya kai dalar Amurka biliyan 750, wanda akasarinsu ne aka zuba wa kasashen da ke Latin Amurka da yankin Caribbean da kasashen Afrika.
Haka kuma, bisa kididdigar da aka samu a gun taron UNCTAD, an ce, yawan jarin kai tsaye da aka zuba ma kasar Sin a bara ya kai dalar Amurka biliyan 127, kuma ya kai matsayi na 2 a duniya.(Bako)