Shugaban Bankin bunkasa hada-hadar safara na nahiyar Afirka ko Afrexim a takaice, Jean-Louis Ekra, ya ce kasashen Afirka sun samu saurin bunkasuwar tattalin arziki, inda gagarumar gudummawar da kasar Sin ta bayar ta kasance daya daga dalilan ci gabansu, irin gudummawar da ba za a iya mantawa da ita ba.
Ekra wanda ya bayyana hakan a 'yan kwanakin baya, yayin taro da aka shirya kan ma'adanai masu daraja a birnin Dubai a karo na uku, ya ce kusan dukkan kasashen Afirka, suna cin moriyar ayyukan da kamfanonin kasar Sin suka zuba jari cikin su, wadanda suka taka muhimmiyar rawa wajen farfadowar tattalin arzikin nahiyar ta Afirka.
Ya ce sakamakon taimakon da kasar ta Sin ta baiwa nahiyar ne, ya sa Afirka ta zama wani yanki da ya fi samun saurin bunkasuwa a duk duniya. Baya ga Asiya, har ma nahiyar ta tabbatar da karuwar tattalin arziki da kaso 3.4 bisa dari, duk da yanayin rikicin tattalin arziki na duniya a shekarar 2009.
Mista Ekra ya kuma ce a halin yanzu, kason hada-hadar kudin Bankin na Afrexim, da cibiyoyin hada-hadar kudin Sin ke rike da su, ya kai kashi 3 bisa dari, adadin da ya ninka sau daya bisa na baya. Haka kuma, bangarorin biyu suna ci gaba da shawarwari cikin yakini, domin kara yawan kason da Sin ke da shi a bankin. (Danladi)