Kasar Afrika ta Kudu ta yi maraba da sanarwar daga matsayin Najeriya, kasa mafi yawan al'umma a nahiyar Afrika, a sahun gaba ta fuskar karfin tattalin arziki a shiyyar kasashen dake kudu da hamadar Sahara, in ji bitalmanin kasar Afrika ta Kudu a ranar Talata.
Sanarwar tana amsa sakon yau da kullum na Afrika ta Kudu tun a shekarar 1994 na cewa, muna fatan ganin karin tattalin arzikin Afrika na karuwa da kuma amfanawa arzikinsu, in ji bitalmanin kasar a cikin wata sanarwa.
Najeriya ta zama kasa mafi karfin tattalin arziki a Afrika tun lokacin da kasar ta sake duba tsarin bayananta na GDP, yawan kudin da aka samu daga sarrafa dukiyar kasa. Wato a da, ba a bayyana yawan kudin da aka samu wajen bangarorin sadarwa, fasahohin zamani, kide-kide, sayarwa ta hanyar internet, kamfanonin jiragen sama da bunkasuwar sana'ar shirya fina finai a kasar ba.
GDP din wannan kasa dake yammacin Afrika a shekarar 2013 ya kai Naira triliyan 80,3, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 509,9 idan aka kwatanta da dalar Amurka biliyan 370,3 a karshen shekarar 2013 na kasar Afrika ta Kudu, a cewar hukumar kididdiga ta Najeriya. (Maman Ada)