Dangane da lamarin, Yao Jian, kakakin ma'aikatar harkokin kasuwancin kasar Sin ya yi jawabin cewa, a matsayinta na kasa mai tasowa, kasar Sin ta zama ta farko a duniya a fannin cinikayyar hajoji, lamarin da ya kasance tamkar wata sabuwar ishara ce gare ta a fannin bunkasa cinikayyar waje, haka kuma wani muhimmin sakamako ne da Sin ta samu ta fuskar yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje da kuma shiga ayyukan raya tattalin arzikin duniya waje guda cikin himma. Yanzu kasar Sin tana matsayin abokiyar cinikayya mafi girma ga kasashe da yankuna fiye da 120 a duniya, tana samar wa abokan cinikinta na kasa da kasa dimbin guraben aikin yi da kuma damar zuba jari.
Duk da haka mista Yao ya nuna cewa, ko da yake kasar Sin na kan gaba a fannin cinikayyar hajoji tsakanin kasa da kasa, amma akwai jan aiki a gaban ta wajen kyautata karfinta na yin cinikayya. (Tasallah)