Rahotanni daga jihar Lagos dake tarayyar Najeriya, na cewa, an bude babban taron tattauna batutuwan da suka jibanci tattalin arzikin kasar karo na 10 a ranar Litinin, mutane sama da 500 suka halarci taron.
A cewar babban daraktan shirya taron na wannan karo Marienne Mazou, taron mai taken "mai da bunkasuwa hanyar amfana daga damammaki" zai mai da hankali ne, kan nazartar tasirin Najeriyar a fagen tattalin arzikin duniya.
Mazou ya ce, Najeriya da ke sahun gaba, wajen yawan masu sha'awar zuwa jari daga ketare, na ci gaba da fuskantar kalubale da dama, ciki hadda batun tsaro, da talauci da kuma matsalar jagoranci.
Da yake tsokaci ga kamfanin dillancin labaran kasar Sin Xinhua kan manufar taron, wakilin kasar Sin a taron, kuma jakadan kasar mai lura da batutuwan da suka jibanci Afirka Zhong Jianhua ya ce, ya lura da yadda aka mai da hankali kwarai kan batun fadada samar da damammakin ci gaba.
Ya ce, duk da ci gaban da Najeriya ke samu karkashin manufofin gwamnati na sauye-sauye, a hannu guda akwai bukatar mahukuntan ta su zage damtse, wajen inganta hanyoyin zuba jari, ta yadda hakan zai dace da kudurin bunkasa kasar. (Saminu)