Bugu da kari, Sin wadda ta zurfafa yin kwaskwarima da samun wadata za ta samarwa duniya zarafi a bangarorin daban-daban, ciki hadda kasuwanni, zuba jari, samun bunkasuwa da hadin kai. Ban da haka, inji shi, kasar za ta ba da gudumawarta ga zaman lafiyar duniya. Ministan harkokin wajen na kasar Sin har ila yau ya bayyana cewa, Sin za ta nace ga hanyar samun bunkasuwa cikin lumana, a sa'i daya kuma za ta ci gaba da sa kaimi ga kasa da kasa na ganin sun bi hanyar samun bunkasuwa cikin lumana, tare kuma da daukar karin nauyin kasa da kasa, har da kokarin shiga tsakanin wasu manyan matsalolin da suke fi jawo hankali, sannan kuma zata ci gaba da warware rikici da bambancin ra'ayi ta hanyar sulhuntawa cikin daidaici, gami da kiyaye mutuncin bil Adam da doka da daidaituwar kasa da kasa.
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da burin da Sin za ta cimma na farfado da al'ummarsu mai jigon "mafarin kasar Sin", in ji shi, kwaskwarimar da Sin za ta yi a sabon zagaye za ta taimaka ga cimma wannan buri. (Amina)