in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
IMF ya rage hasashen bunkasar tattalin arzikin duniya
2014-04-09 09:48:58 cri

Asusun ba da lamuni na IMF ya rage hasashen da ya yi, na irin bunkasar tattalin arzikin da za a samu a duniya a bana, da kuma shekarar 2015 mai zuwa da kaso 0.1 bisa dari.

Hakan dai na nufin a wannan shekara ta 2014, bisa hasashen na IMF, tattalin arzikin duniya zai samu karuwa ne da kaso 3.6, Yayin da kuma a shekarar 2015 mai zuwa zai karu da kaso 3.9 bisa dari.

Bugu da kari hasashen na wannan karo ya nuna cewa, tattalin arzikin kasashe masu saurin samun bunkasuwa, da na kasashe masu tasowa ne ke ci gaba da samar da kaso biyu bisa uku, na bunkasar tattalin arzikin duniya.

Duk da sauyin da aka samu game da wannan hasashe, IMF ya ce, hasashen ci gaban kasar Sin na kaso 7.5 bisa dari a bana, da kaso 7.3 a badi, bai canza ba.

A cewar IMF, harkokin tattalin arziki sun bunkasa tun daga watanni shidan karshen shekarar bara, ana kuma sa ran kara habakar su a bana da kuma badi. Har wa yau asusun ya ce, duk da irin ci gaban da ake gani a wasu sassa, a hannu guda kalubalen yiwuwar samun koma baya na tattare da tattalin arzikin duniya. Don haka IMF ya baiwa kasashe masu tasowa shawarar yin shirin kaucewa tasirin hakan. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China