A cikin wani rahoto da babban bankin duniya ya gabatar a ranar Litinin, an ce, tattalin arzikin kasashen Afrika dake kudu da Sahara, na ci gaba da kasancewa a cikin karfin shi, to amma rahoton bankin duniyar ya ce, wannan bunkasar tattalin arzikin da ake samu na fuskantar kalubale na karancin farashin kayayyaki masarufi da kuma koma bayan da ake samu a bangaren uwar kudin da ake juyawa.
A cikin rahoton bankin duniyar na kwanan nan a kan ci gaban tattalin arzikin Afrika, babban bankin dunyar ya ce, a shekarar ta 2013, yawancin kasashen Afrika dake kudu da Sahara sun sami gaggarumin habbaka na harkokin tattalin arziki, a inda daga kashi 4.7 bisa dari a shekara ta 2013, ya zuwa kashi 5.2 bisa dari a shekara ta 2014, duk da yake cewar, an samu wadansu canje-canje masu ma'ana a yawancin kasashen.
Rahoton na bankin duniyar mai taken "bugun zuciyar Afrika" ya ce, bukatu na cikin gida da saka jari a bangaren albarkatun kasa da samar da ababen jin dadin rayuwa gami da bukatun jama'a za su ci gaba da zaburar da habbakar tattalin arzikin a yawancin kasashen dake yankin.
Rahoton na bankin duniya, mai hedkwata a birnin Washington ta Amurka, ya yi gargadi cewar, duk da yake ana sa ran tattalin arziki na kasashen Afrika da ke kudu da Sahara, ya ci gaba da kasancewa da karfinsa fiye da sauran kasashe masu tasowa da yawa na duniya, to amma habbakar tattalin arzikin zai kasance ne a cikin barazana na faduwar farashin kayayyakin masarufi da kuma rashin tabbas na farashin kayayyakin abinci gami da halin rashin tabbas na siyasa. (Suwaiba)