Hukumar kididdiga ta kasar Ghana (GSS) ta sanar a ranar Laraba cewa, cigaban tattalin arzikin kasar Ghana, bisa binciken alkaluma ya kai kashi 7,1 cikin 100 a shekarar 2013, bayan karuwar tattalin arzikin kasar da kashi 8,8 cikin 100 a shekarar 2012.
Bangaren aikin ba da hidima ya samun karuwa mafi girma ta kashi 8,9 cikin 100, sannan bangaren masana'antu kashi 7 cikin 100, a yayin da bangaren noma ya samu kashi 5,2 cikin dari wanda ya kasance adadi mafi karanci.
Aikin ba da hidima ya kasance bangare mafi muhimmanci, wanda ya taimakawa GDP din kasar kusan da kashi 49,5 cikin 100 a shekarar 2013 idan aka kwatanta da na shekarar 2012 dake kashi 48,84 cikin 100, in ji jami'in hukumar GSS mista Philomera Nyarko. (Maman Ada)