Shugaba John Dramani Mahama na kasar Ghana, ya ce, nan da 'dan lokaci kankane, matsalolin da suka dabaibaye tattalin arzikin kasarsa za su zama tarihi.
Mahama ya bayyana hakan ne jiya Talata, yayin da yakewa majalissar dokokin kasar jawabi kan halin da kasar ke ciki. Ya ce, duk da cewa matakan da gwamnati ke dauka na tattare da matsi, a hannu guda cikin kankanen lokaci, za su haifar da burin da ake da shi na daidaitar al'amura.
Shugaban ya kara da cewa, akwai tarin dalilai da suka haifar da kalubalen da ake fama da shi, ciki hadda batun matsalar tattalin arzikin duniya da ta shafi kowa, da matakan da manyan kasashen duniya ke dauka na saita yanayin tattalin arzikinsu, da ma matakan da ake dauka a gida domin kamo bakin zaren.
Cikin manyan dalilai da suka sanya Ghana shiga halin da take ciki a gida, a cewarsa, akwai batun daukar matakan saita tattalin arziki, da aiwatar da dokar karin albashi mai gwabi, da tallafin man fetir da kasar ke samarwa. Matakan da suka haifar da gibin kusan kaso 12 bisa dari a kasafin kudin kasar, da hauhawar farashi da ya kai kaso 13 bisa dari, tare da karuwar kudin ruwa da basukan da ake bin kasar.
Duk dai da wadannan tarin kalubale, shugaba Mahama ya yi imanin cewa, tattalin arzikin kasar na da k